<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>267</hymn_number>
<title>Ko Zan Tafi da Hannu Wofi LW267</title>
<lyrics>[V1]
 1) Ko zan tafi da hannu wofi
 Wurin Ubangijina?
 Ba mai tuba da zan kawo
 Ran da na ga fuskarsa?

[C1]
   In na tafi da hannu wofi,
   Babu kowa tare da ni,
   Ran da na ga fuskar Yesu
   Lalle kunya ce zan ji.

[V2]
 2) Ubangiji ya sha wahala
 Garin neman tumaki,
 Har ya ba da ransa duka
 Ni Mai Bi fa, me zan yi?

[V3]
 3) Ƴanuwana ma sun tashi
 Suna gama aikinsa.
 Ga ni nan mai hannu wofi
 Ni kuwa ban yi aiki ba.

[V4]
 4) Ni ma ina so in tashi
 Cikin ƙarfin ikonsa,
 Don in sami masu tuba
 Da zan Kawo wurinsa.</lyrics>
</song>